IQNA

Kashi Daya Bisa Uku Na ‘Yan Ta’addan ISIS Daga Turai Suke

22:02 - September 08, 2014
Lambar Labari: 1448186
Bangaren kasa da kasa, kungiyar musulmi marassa rinjaye a kasar Spain ta fitar da wani bayani da ke cewa kimanin kasha daya bias uku na ‘yan ta’addan da ke yaki karkashin inuwar kungiyar Daesh sun fito ne daga kasashen nahiyar turai.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babbar kungiyar musulmi marassa rinjaye a kasar Spain ta fitar da wani bayani da ke cewa kimanin kasha daya bias uku na ‘yan ta’addan da ke yaki karkashin inuwar kungiyar Daesh sun fito ne daga kasashen nahiyar turai zuwa kasashen Syria da kuma Iraki inda ‘yan ta’addan suke ayyukansu.
Yan ta'addan ISIS sun yi wa wasu likitoci biyu mata yankan rago a birnin Mausil na kasar Iraki, bayan da suka ki amincewa su yi wasu 'ya'yan kungiyar maani.   Rahoton da kamafanin dilalncin labaran Saumariyyah News ya bayar ya ce 'yan ta'addan na ISIS sun kai farmaki a jiya aAsabar a kan gidan likitocin biyu, inda suka fito da su a gaban gidajensu a banar jama'a suka yi musu yankan rago, bisa hujjar cewa an kai wasu 'ya'yan kungiyar da suka samu raunuka a musayar wuta da sojojin Iraki zuwa asibitin da suke aiki, amma suka ki yi musu magani, a kan haka kungiyar ta yanke musu hukuncin kisa kuma ta aiwatar da shi.  
A cikin makon da ya gabata ma 'yan ta'addan na ISIS sun kashe wata mata likita har lahira ta hanyar bude wutar bindiga a kanta, bisa hujjar cewa ba ta saka nikabi. Rahoton ya ce 'yan ta'addan na ISIS sun ki su mika gawawwakin likitocin mata da suka kashe ga danginsu domin yi musu janaza.
1448009

Abubuwan Da Ya Shafa: spain
captcha