IQNA

Gidan Radiyon Kur'ani Na Masar Na Watsa Shiri kan Aikin Hajji

22:38 - October 02, 2014
Lambar Labari: 1456514
Bangaren kasa da kasa, gidan radiyon da ke watsa shirinsa kan harkokin kur'ani mai tsarki a kasar Masar da ake kira radio kur'ani yana watsa shiri danagen da ayyukan hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbarul cewa, daga yau gidan radiyon kur'ani na Masar yana watsa shiri dangane da ayyukan hajjin bana kai tsaye.

A wani rahoto da bayar a kimanin mahajjata miliyan uku ne suka fara gudanar ayyukan hajji a yau, inda suka isa Mina, a gobe Juma'a kuma za a gudanar da ayyukan ranar Arafah.

Rahotanni daga kasar ta Saudiyyah sun ce alhazan suna ci gaba da isa Mina kuma komai yana tafiya lami lafiya, yayin da wasu rahotanni da jaridar Al-riyadh ta bayar sun ce 'yan sa'oi kafin fara isar alhazai a safiyar a Mina, wasu daga tantunan da aka kafa sun kama da wuta, amma 'yan kwanakwana sun kashe wutar kafin ta isa ga sauran tantunan, kuma babu wanda ya rasa ransa ko samun rauni.

Hukumomin na Saudiyyah dai ba su karin bayani da musabbabin tashin wanann gobara a Mina ba, amma dai shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na kasar As'ad Muhammad Bin Usman ya ce ma'aikatansa sun kammala daukar dukkanin matakai domin kare rayuka da lafiyar dukkanin mahajjata.

1455895

Abubuwan Da Ya Shafa: radio
captcha