IQNA

Jagororin Addinai A Faransa Sun Suka Kan yin Amfani Da addini Domin Kamfe Na Siyasa

16:42 - March 19, 2012
Lambar Labari: 2293778
Bangaren kasa da kasa, malaman addinai a kasar Faransa sun yi kira da a daina yin amfani da addini domin kamfe na siyasa wanda a cewarsu hakan bai dace da kasa da ke ikirarin bin tafarki na demokradiyya ba.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo cewa, malaman addinai a kasar Faransa sun yi kira da a daina yin amfani da addini domin kamfe na siyasa wanda a cewarsu hakan bai dace da kasa irin faransa ba, kuma za su ci gaba da fadaar da jama'a kan hakan.
Wasu rahotanni daga kasar Faransa sun habarta cewa, da safiyar yau ne aka kai wani hari kan wata makarantar yahudawa da ke garin Tuluse na kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.
Babban mai shigar da kara na kasar Faransa Micheal Faley ya sheda cewa, daga irin bayanan da suka samu wani mutum ne a kan babur ya bude wutar bindiga kan makarantar da yahudawa da ke cikin garin na Tuluse, kuma sun samu bayanin mutuwar mutane uku ne bayan faruwar lamarin, amma daga bisani adadin ya kai mutane hudu da suka hada da kananan yara uku, ya ce yanzu haka jami'an tsaro sun shiga gudanar da bincike kan wannan lamari.
A nata bangaren haramtacciyar kasar Isra'ila ta nuna matukar kaduwa dangane da kai wannan hari da aka yi kan makarantar yahudawa, duk kuwa da cewa an kai harin ne bayan 'yan sa'oi da sojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar da hare-hare kan palastinawa fararen hula da ke yankin Rafah a kudancin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar wasu kananan yara. 973786
captcha