IQNA

Isra'ia Ta Rusa Wasu Daga Cikin Muhimamn Wuraren Tarihi A Birnin Qods

17:59 - June 27, 2012
Lambar Labari: 2356043
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara rusa wasu daga cikin muhimamn wurare masu tsarki da ke cikin birnin Qods a matsayin wani mataki na tsokanar musulmi da kuma mabiya addinin kirista wadanda suke girmama wurare masu tsarki da ke birnin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara rusa wasu daga cikin muhimamn wurare masu tsarki da ke cikin birnin Qods a matsayin wani mataki na tsokanar musulmi da kuma mabiya addinin kirista wadanda suke girmama wurare masu tsarki da ke birnin an Qods mai alfarma.
A wani abarin kuma rahotanni daga kasar Syria sun habarta cewa 'yan ta'addan kasar da ke samun goyon baya daga Amurka da sauran kasashen yammacin turai, sun kaddamar da wani harin bam a yau da rana tsaka a kan gidan talabijin din Al-Ikhbariyyah mallakin gwamnatin kasar.
A cikin wani bayani da ma'aikatar watsa labaran Syria ta fitar kasa da sa'oi biyu da suka gabata, ta tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne da bama-bamai, kuma suka tsare wasu daga cikin ma'aikatan talabijin a cikin wani daki suka bude wutar bindiga a kansu, a nan take suka kashe injiniyoyi uku da suke aiki da talabijin din.
A bangare guda kuma wasu rahotannin sun tabbatar da cewa an yi musayar wuta mai tsanani tsakanin 'yan ta'adda da kuma dakarun gwamnati a wasu yankuna da Dauma da kuma Dai Al-zur, inda inda dakarun gwanati 10 suka rasa rayukansu, yayin da 'yan ta'adda 116 suka halaka kuma aka kame wasu masu tarin yawa, daga cikinsu har da 'yan alakaida da suka shigo kasar ta barauniyar hanya daga wasu kasashen larabawa, musamman daga kasashen Saudiyya, Kuwait Libya da kuma Tunisia.
1038799




captcha