IQNA

Wasu Musulmi Sun Yi Sallar Juma’a A Jiya A gaban Fadar White House

17:33 - February 14, 2015
Lambar Labari: 2849622
Bangaren kasa da kasa, daruruwan musulmi sun gudanar da sallar juma’a a jiya gaban fadar white house da ke kasar Amurka domin nuna rashin amincewarsu da abin da aka yin a kashe musulmi a jahar North Carolina.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Islam.az cewa, a jiya wasu daruruwan mabiya addinin muslunci mazauna Amurka sun gudanar da sallar juma’a  gaban fadar white house kuma fadar shugaban kasar domin nuna rashin amincewarsu da abin da aka yin a kashe musulmi a jahar North Carolina saboda tsanar musulunci.

A bangare guda kuma duk ajiyan wasu mutane ne suka gudanar da jerin gwano a birnin washington domin nuna rashin amincewarsu da nuna halin ko in kula da gwamnatin kasar ta yi kan kisan da aka yi wa wasu daliban jami'a uku dukkaninsu musulmi kisan gilla a jahar Carolina ta arewa. 

Wasu rahotanni sun ce masu gangamin sun cika wasu manyan tituna a birnin Washington,a  cikinsu akwai musulmi da wadanda ba musulmi ba, da suke neman a bi kadun hakkin mutanen da aka kashe bisa zalunci.

Mutanen uku sun rasa rayukansu a lokacin da wani mutum mai kiyayay da su ya bude wutar bindiga a kansu a yankin chapel hill, a wani gidan kwanan dalibai na jami'ar.

2849576

Abubuwan Da Ya Shafa: washington
captcha