IQNA

Kare Masallacin Aqsa Shi Ne Wajibi Ba Yaki A Kan Yemen Ba

23:25 - November 29, 2015
Lambar Labari: 3458403
Bangaren kasa da kasa, limamin masallacin Aqsa ya soki lamirin mahukuntan kasar Saudiyyah dangane da kisan kiyashin da suke yi kan al’ummar kasar Yemen a daidai lokacin da suka manta da masallacin Aqsa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sabanet cewa, Sheikh Salahuddin Abu Arafah limamin masallacin Aqsa ya yi kakakusar suka kan mahukuntan kasar Saudiyyah dangane da kisan kiyashin da suke yi kan al’ummar kasar Yemen, inda y ace sun manta da masallacin Aqsa suna kashe musulmi a Yemen.

Ya ce a daidsai lokacin da kuke kashe al’ummar kasar Yemen mutane da dama ne suke mutuwa a Palastinu a karkashin harsasshin yahudawan sahyuniya da makamansu da jiragensu, shin ina karfink da kuke da shi da kuke kashe mutanen Yemen ba za ku iya kare palastinawa da shi ba.

Abu Arafah ya ci gaba da cewa babbana bin takaici ne yadda mahukuntan kasar Saudiyya suka zama tamkar rakmi da aka la a hannun turawa wajen kare manufofinsu, ta yadda babban abin da ke  agabansu shi ne aiwatar da manufofin trawa tare da kare yahudawa.

Dangane da hakan ya kara da cewa harin da Saudiyya take kaiwa kan al’ummar kasar Yemen, shi ne ya kara ma Isra’ila karfin gwiwa wajen ci gaba da tasa kan al’ummar Palastinu tare da ci gaba da yi musu kisan kiyashi hankali kwance.

Ya kara da cewa, irin makaman da Saudiyya ta yi amfani da su kan a’ummar kasar Yemen wajen rusa makarantu da masallatai da asibitoci, da a ce ta yi amfani da su kan Isra’ila ne da masallacin Quds ya samu yanci daga mamayar yahudawa.

3458182

Abubuwan Da Ya Shafa: quds
captcha