IQNA

Ku Yi Mu’amala Da Musulmi Da Bisa Masaniya Ta Hakika Kuma Ta Gaskiya

23:29 - November 29, 2015
Lambar Labari: 3458407
Bangaren siyasa, a cikin sakon da jagoran juyin juya halin muslunci ya aike zuwa ga matasan kasashen yammacin turai ya bayyana cewa, yana kira gare su da su amfani da hakikanin koyarwar muslunci wajen sanin addinin muslunci, kuma su amfana da gogewa da masaniya da musulmi suke da ita.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, a cikin sakon da jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei ya aike zuwa ga matasan nahiyra turai, ya ja hankalinsu kan su lura da yadda ake yi amfani da ta’addanci wajen saka Katanga a tsakaninsu da fahimtar addinin mulusnci.

Ga matanin Sakon Kamar Haka:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai

Ga Dukkanin Matasan Kasashen Yammaci.



Harin ta’addancin rashin imani da sosa rai da ya faru a kasar Faransa, shi ne ya sake sanya ni yin magana da ku, matasa. Lalle abin bakin ciki ne yadda wadannan abubuwan suke faruwa da kuma janyo magana, to amma hakikanin lamarin shi ne cewa matukar wannan lamari mai bakanta rai bai share fagen samar da mafita da kuma yin tunani bai daya (na magance wannan matsalar) ba, to kuwa za a fuskanci hasara ninkin ba ninkiya. Cutuwa da wahalar kowane irin mutum, a ko ina yake a duniyan nan, a kan kanta wani abin bakin ciki da sosa ran sauran bil’adama ne. Ganin mutuwar karamin yaro a gaban masoyansa (iyaye ko ‘yan’uwansa), ko mutuwar wata mahaifiya da hakan ke mayar da farin cikin iyalanta zuwa ga wani yanayi na juyayi, ko mijin da ke dauke da gawar matarsa zuwa wani waje cikin bakin ciki, ko kuma dan kallon da bai san cewa nan gaba kadan ko zai ci gaba da rayuwa ko a’a ba, ko shakka irin wadannan yanayi ne masu sosa rai da zukatan mutane. Duk mutumin da yake da komai kashin kauna da dan’adamtaka, lalle zai tasiransu da kuma jin zafin ganin irin wannan yanayin, shin hakan a Faransa ne ya faru ko kuma a Palastinu ko Iraki ko Labanon ko Siriya. Ko shakka babu musulmi biliyan guda da rabi (na duniya) suna jin zafin faruwar irin wannan yanayin, sannan kuma suna gaba da kuma kiyayya da masu aikata wannan danyen aiki da kuma masu daure musu gindi. To amma lamarin shi ne cewa matukar irin wadannan cutarwa da wahalhalu ba su zamanto dalilin da za su sanya a gina makoma mai kyau da samun kwanciyar hankali ba, to kawai za a takaita ne ga tunanin abubuwan da suka faru masu sosa rai kana kuma maras amfani. Ni na yi amanna da cewa ku din nan matasa kawai, ku ne ta hanyar daukar darussa daga abubuwa marasa kyau da suke faruwa a halin yanzu, za ku iya samar da sabbin hanyoyin gina gobe da kuma kawo karshen irin mummunan rashin tabbas din da kasashen yammaci suka sanya (duniya) a ciki.

Ko shakka babu a yau ta’addanci ya zamanto wata cuta da bala'i da muka yi tarayya cikinsa mu da ku, to amma ya zama wajibi ku san cewa akwai bambanci guda biyu na asali tsakanin rashin tsaro da zaman dardar din da kuka shiga ciki sakamakon harin baya-bayan nan, da kuma wahalhalun da al’ummomin kasashen Iraki, Yemen, Siirya da Afghanistan suke ciki tsawon shekaru. Na farko shi ne cewa kasashen musulmi sun jima ainun cikin irin wannan tashin hankali kuma a bangarori daban-daban. Na biyu kuma shi ne cewa abin bakin ciki irin wannan tashin hankali da kashe-kashe sun kasance ne karkashin kula da kuma goyon bayan wasu manyan kasashen duniya ta hanyoyi daban-daban. A yau dai da kyar za ka sami mutumin da ba shi da masaniya kan hannun da Amurka take da shi wajen kirkira ko kuma karfafawa da bada makamai ga kungiyoyin Al-Ka’ida, Taliban da sauran ‘yan amshin shatansu. Baya ga wannan goyon baya na kai tsaye, har ila yau kuma sun kasance kawaye kuma masu goyon bayan (kasashen) da suke goyon bayan (kungiyoyin) ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi duk kuwa da tsarin kama-karya da suke gudanarwa a (kasashensu). A daidai lokacin da suke ci gaba da takurawa da kuma matsin lamba wa masu riko da mafi ci gaba da riko da tsarin da ya samo asali daga tsarin demokradiyya a wannan yankin. Siyasa da mu’amalar harshen damo da kasashen yammaci suke yi ga kungiyoyi masu neman ‘yanci a duniyar musulmi wani babban misali ne na irin karo da juna da ake samu cikin siyasar kasashen yammaci.

Wata fuska wacce ta ke nuni da wannan irin cin karon, ita ce  goyon bayan da ake nunawa ta’addancin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Mutanen Palasdinu wadanda ake zalunta sun rika fuskantar na’uoi daban-daban na ta’addanci a tsawon shekaru sittin.

Idan sai a wannan lokacin ne mutanen turai su ke fakewa a cikin gidajensu na wani kwanaki, da nisantar shiga cikin taruka, to iyalan palasdinawa hatta a cikin gidajensu basu da aminci daga kisa da ta’addin tsarin Sahayoniya.

A wannan lokacin da wane irin amfani da karfi da kuma kekashewar zuciya za a iya kwatanta da gine-ginen share wuri zauna da ‘yan sahayoniya su ke yi.? Kuma  ko kadan kawayen wannan haramtacciyar hukumar  da su ka fi tasiri akanta ba su ladabtar da ita, ko kuma daga wajen kungiyoyin  kasa da kasa wadanda a zahiri ne su ke da ‘yanci.

A kowace rana ta Allah ana rusa gidan palasdinawa  ko kuma lambuna da gonakinsu, maimakon ace suna basu damar samar da abubuwan kyautata rayuwa ko kuma na tattara amfanin gona. Kuma mafi rinjaye dukkanin wadannan abubuwan na nuna kekeshewar zuciya suna faruwa ne a idanun mata da kananan yara, wadanda su ke ganin yadda ake dukan iyalansu da kuma yadda ake tafiya da su wajen azabtarwa. Shin ko kun san wani ko wata kekashewar zuciya wacce ta kai girman wannan zamanin?

Kashe mace akan titi saboda kawai ta nuna turjiya ga sojan da ya yi jigida da makamai. Idan wannan ba ta’addanci ba ne to menene?

Saboda sojojin wata daula ce ta mamaya ta ke aikata wannan irin dabbancin bai kamata a kira shi wuce gona da iri ba?

Watakila saboda an dauki shekaru 60 ana maimata  nuna hotunan wannan abin ne a telbijin ya sa ba su motsa mana zukata?

Aikewa da sojoji zuwa kasashen musulmi a shekarun bayan nan, da su kansu suna a matsayin ragunan layya ne, yana nuni ne da tunanin turawa mai cin karo da juna. Kasashen da ake kai wa harin, baya ga dimbin asarar da ake yi musu ta fuskar, mutane aka kuma tafka musu wasu asarorin ta fuskokin manyan cibiyoyin tattalin arziki da masana’antu. Ana kuwa kawo musu tsaiko da cikas wajen ci gaban masana’antunsu. A wasu fuskokin ana maida su baya zuwa shekaru masu yawa. Amma kuma duk da haka suna bukatar da kada su dauki kawukansu a matsayin wadanda aka zalunta. Ya za a ce kasar da aka rusa sannan kuma aka maida birananta zuwa kufai, amma kuma a bukace su kada da dauki kawukansu a matsayin wadanda aka zalunta. Ashe maimakon ace an bukaci shafe musifun da su ka faru, bai dacewa ba a nemi gafara ba?

Wahalhalun da kasashen musulmi su ka fuskanta a cikin shekarun bayan nan da kuma kokarin yi wa fuskar mahara kwaskwarima, bai gaza da  asarar da aka yi ba.

Ya ku matasa! Ni ina da fatan cewa, a nan gaba za ku canja wannan gurbataccen tunanin, tunanin da aka gina shi kan bakaken manufofi boyayyu da nufin cutar da wasu. A ganina mataki na farko na samar da tsaro da kwanciyar hankali shi ne yin gyara da kuma daidaita wannan tunani da ke jawo tashin hankali. Matukar dai siyasar kasashen yammacin turai mai harshen damo za ta ci gaba da jagoranci, kuma ta’addanci da masu daukar nauyinsa suna ba shi kariya za su ci gaba da raba shi zuwa gida biyu, mai tsanani da mai sassauci, matukar za a ci gaba da fifita amfanin da kasashe suke samu a kan ‘yan adamtaka, to bai kamata a nemi warware matsalar da ake kuka a kanta a  wani wuri na daban ba.

Abin ban takaici shi ne wannan salon ya dauki tsawon shekaru a hankali a hankali yana samun wurin zama  a cikin siyasar kasashen yammacin turai, ta yadda ya haifar da mummunar illa a boye a cikin wannan salon siyasa. Da dama daga cikin kasashen duniya suna alfahari da al’adunsu na iyaye da kakanni, al’adun da suka karfafa kyakyawar dangantaka a tsakanin al’ummomin bil adama, duniyar Musulunci ba a bar ta a baya ba ta wannan fuska. Amma yau a wannan zamanin, duniyar yammaci tana amfani da irin ci gaba da ta samu na zamani domin rusa al’adu da kyawawan dabi’un sauran al’ummomi na duniya ko ta wace hanya. Ni ina ganin kallafa al’adun yammacin duniya a kan sauran al’ummomi, da tozarta al’adu masu ‘yanci da asali, shi kansa wani bangare ne na haifar da fitina, domin kuwa yana tattare da cutarwa ga al’ummomi.

Tozarta manyan al’adu da koyarwar al’ummomi da wasu bangarori na abubuwan da suke girmamawa kuwa, yana zuwa ne a daidai lokacin da al’adun da ake son a maye gurbinsu da su ko alama ba su cancanci hakan ba ko ta wace fuska. A matsayin misali, abubuwa guda biyu; cin-zalun da rashin kyakkyawar dabi’a, wadanda abin takaici sun zama muhimman abubuwan da aka mayar da asasin rubuce-rubucen nahiyar turai a kansu, hakan ya sanya hatta a tsakanin al’ummomin wadannan kasashe karbuwar wannan salo tana raguwa matuka. Abin tambaya a nan shi ne, shin idan muka ce ba mu son wata al’ada maras kyau maras ma’ana shin mun yi laifi? Idan muka hana shigowar wasu al’adu masu yaduwa a tsakanin matasa da rusa tarbiyarsu, shin mun yi laifi? Ni ba ina musun muhimmancin da matsayin al’adu ba ne ga baki daya. Irin wannan yana da yanayi da ake karbarsa idan ya zama mai amfani a cikin rayuwar jama’a da kuma ci gabansu a matsayin al’umma. Amma idan a ka karbi al’adu marassa dacewa da yanayin al’umma sukan zama dalili na babbar asara. Dole ne mu fadi a cikin takaici cewa, kungiyoyi irin su Daesh suna daga cikin irin al’adun da aka shigo da su aka kuma shuka su suka tsiro a cikin al’umma wadanda suke a matsayin asara a cikin al’umma. Domin idan da abin da irin wadannan mutane suke yi yana da alaka ne da akida, to da an ga irin hakan tun kafin kunnowar kan ‘yan mulkin mallaka a cikin duniyar musulmi, alhali tarihi yana nuna sabanin haka ne. Akwai dalilai masu tarin yawa na tarihi da suke bayyawa a fili, dangane da yadda mulkin mallaka ya saka tsattsauran ra’ayi da wuce gona da iri a cikin kwakwalwar wata kabilar kauye a wannan yankin. Ta yaya zai yiwu daya daga cikin addinan da suka fi koyar da dan adam kyawawan dabi’u da ‘yan adamtaka, wanda a cikin matanin kundinsa ya bayyana cewa kashe ran mutum daya daidai yake da kashe dukkanin ‘yan adam, kuma har a samu wata shara kamar Daesh ta fito daga wannan addinin?

A daya bangaren dole ne a yi tambaya kan cewa, me ya sanya wadanda aka haife su a cikin nahiyar turai, suka girma a can suke tunanin addini a can kuma suke shiga cikin wadannan kungiyoyi? Shin zai yiwu kuwa a amince da cewa saboda wani ya yi tafiya sau daya ko sau biyu zuwa wani guri da ake fama da yaki, kawai sai ya koma mutum mai matsanancin ra’ayi yana yin ruwan harsasan bindiga kan ‘yan kasarsa? Tabbas bai kamata a manta da tasirin rayuwa a cikin al’adu marassa kyau da kuma gurbatacciyar zamantakewa da ke haifar da bakin hali na son tashin hankali ba. A nan dole ne a yi bayani, bayanin da zai fito da abin da aka boye a cikin rayuwa ta zamantakewa. Mai yiwuwa ko akwai kiyayya mai zurfi da take komawa zuwa ga lokacin da turawa suke kokarin mikewa ta fuskar bunkasa tattalin arziki da masana’antu, sakamakon nuna bambanci da wariya a tsakanin mutane da rashin adalci ta fuskar shari’a, wanda ya sanya wasu zukatan suke dauke da wannan haushi da takaici, kuma wani abu mai sosa zuciya zai iya tayar da tsohon takaici.

Ko ma dai yaya lamarin yake, ku ne ya zama wajibi a kanku ku warware zaren da ya yi muku dabaibayi, ku cire duk wani kulli da ke cikin ranku, maimakon kara zurfafa baraka sai ku dunke ta, babban kure da aka tafka a  kan batun yaki da ta’addanci shi ne matakan martanin gaggawa, wanda kuma shi ne ya kara fadada baraka dake akwai yanzu.

Duk wani yunkuri da zai saka musulmi mazauna nahiyar turai da Amurka wadanda yawansu ya kai miliyoyi a cikin kunci da takura, kuma da ci gaba da tauye musu hakkokinsu na zamantakewarsu a cikin al’umma fiye da lokutan baya, tare da mayar da su saniyar ware a cikin al’umma, hakan ba wai kawai ba zai warware matsalar ba ne, a’a zai jawo wata baraka ne tare da kara fadada ta. Daukar duk wani mataki da martani musamman idan lamari ya shafi bangaren doka, baya ga kara rabuwar da ke akwai da kuma bude wasu kofofi ga wasu rikice-rikice a nan gaba babu abin da zai haifar. Bisa ga wasu labarai da ake samu, a wasu kasashen turai an kafa wasu dokoki na sanya mutanen gari su rika yin leken asiri a kan musulmi. Wannan dabi’a ce ta zalunci, dukkanmu mun san cewa abin da mai zalunci ya yi babu makawa zai dawo a kansa. Bugu da kari a kan haka kuma musulmi ba su cancanci wannan rashin godiya da mayar musu da mummuna ba. Duniyar yammaci ta san musulmi da kyau tsawon karnoni da suka gabata. A wancan lokacin da turawan yamma suka zama baki a kasashen musulmi, sun kyalla ido sun ga dukiyar mai tare da amfana, a lokacin da suka zama kuma su ne masu masafkin musulmi, sun amfana da ayyuka da kuma tunanin musulmi, a mafi yawan lokuta babu abin da suka gani daga musulmi sai kauna da abin yabawa. Saboda haka ya ku matasa, ina son ku gina sahihiyar mu’amala da duniyar musulmi, bisa masaniya ta gaskiya, tare da amfana da ilmantuwa da gogewa mai yawa da musulmi suke da ita. Idan kuka yi hakan nan ba da jimawa ba za ku ga cewa lallai kun yi gini a kan asasi tabbatacce, kuma inuwar natsuwa da tabbaci za ta isa ga maginansa, zai zama aminci da kwanciyar hankali gare su, hakan kuma zai bude kofar fata ta gari a doron duniya.



Sayyid Ali Khamenei

28/11/2015



Sakon jagora na farko zuwa ga matasan turai an aike da shi ne a cikin shekarar da ta gabata

3458369

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha