Kamfanin
dillancin labaran iqna nakalto shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al’alam
cewa, a yau a lokacin da ake gdanar da sallar Juma’a ayau wani bam ya tashi.
Wannan hari
kan masallacin Imam Rida (AS) wasu
mutane da ake zaton masu dauke da akidar Takfiriyyah ne suka kasha wanda masallacin
Juma'a ne kuma a lokacin sallar Juma'a a yau a garin Ihsa'a da yankin
Sharqiyyah.
Garin dai daya ne daga
cikin garuruwan mabiya mazhabar shi'a a gabacin kasar Saudiyya, lamarin da ya
yi sanadiyyar rasuwar masallata uku, yayin da wasu rahotanni ke cewa 5, tare da
jikkata wasu da dama,
Sai masallatan sun
samu sa'ar cafke daya daga cikin maharan, a lokacin da yake shirin tayar da
wata jigidar bama-bamai da ke jikinsa, an kuma mika shi ga jami'an tsaron kasar.
Tashar Ala’arabiyya
wadda mallakin gwamnatin saudiyya ce ta bayar da rahoton cewa an kai harin
wannan masallaci na Imam Rida (AS) kuma an kashe mutane uku tare da jikkatar
wasu.
A nata bangaren tashar
talabijin ta PressTV ta bayar da rahoton cewa an kai wannan hari a lokacin da
ake gudanar da sallar Juma’a a masallacin Imam Rida (AS), kamar yadda kuma aka
kame daya daga cikin maharani, wanda daga bisani jami’an tsaro suka karbe shi.
Bisa ga rahoton da mahukuntan
kasar ta Saudiyya suka bayar, sun tabbatar da cewa an kai wannan hari ne ta
hanyar tayar da bam, da kuma bude wutar bindiga, yayin da kuma daga bisani an
kame daya daga cikin maharan wanda yanzu haka yake hannun jami’an tsaro an agudanar
da bincike kan lamarinsa.
Wannan dai bas hi ne
karon farko da ake kai irin wadannan hare-hare kan mabiya mazhabar shi’a a
yankin gabacin saudiyya ba, wanda kuma yanki ne na mabiya mazhabar shi’a a
gabacin kasar wqanda kuma daga nan Saudiyya take samun dukkanin man fetur da ta
dogara da shi.