IQNA

Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta Harda Da Tajwidi A Kuwait

13:56 - September 25, 2016
Lambar Labari: 3480805
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta harda da kuma tajwidi a kasar Kuwait tare da halartar makaranta.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cwa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Kuwait cewa, Muhammad Aljalahima shi ne babban daraktan kula da ayyukan kur’ani a ma’aikatar kula da harkokin addini shi ne kuma ya sanar da fara aiwatar da shirin.

Ya ce an fara gasar ne tun kimanin shekaru ashirin da suka gabata, kuma tun daga lokacin lamarin yana ci gaba da kara samun ci gaba a dukkanin fuskoki.

Bangarorin da gasar take mayar da hankali kansu dai su ne harda da kuma karatu ta yadda za a iya tantance karfin tajwidi mai karatun, ko kuma tambayoy kai tsaye dangane da hukuncin tajwidi.

An kasa bangarorin gasar ne zuwa manya da kuma matasa, ta yadda hakan zai iya bayar da damar tantance dukkanin bangarorin.

A shekarar bana an fara ne da ‘yan kasar ta Kuwait da suke zaunea kasashen ketare, kuma an fara daga birnin London na kasar Birtaniya.

Abdulrahman Alhashash mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar ya bayyana cewa, sun kebance kudade da suka kai dinari dubu 15 ga duk wanda ya zo na daya, sai kuma wasu kudaden ga wadanda suka biyo baya.

Kowace sekara kimanin masu gasa 2000 ne ke shiga gasar, tun daga fara ta a shkarar 1996 ya zuwa yanzu mutane dubu 600 ne suka shiga.

3532286


captcha