IQNA

Tsohon Shugban Sudan:

Kur’ani Ya Karfafa Zaman Lafiya A Tsakanin Maiya Addinai

23:53 - October 02, 2016
Lambar Labari: 3480818
Bangaren kasa da kasa, Abdulrahman Swar Zahab tsohon shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa kur’ani ya karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Abdulrahman Swar Zahab tsohon shugaban kasar Sudan a gaban taron masana daga cikin musulmi da kuam kasashen yammaci da aka gudanar a birnin Geneva ya bayyana cewa kur’ani ya karfafa zaman lafiya a tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya.

Ya ce ko shakka babu babban zalunci ne a akn addinin muslunci a danganta si da ayyukan tashin hankali, domin kuwa babu inda muslunci yay i kira zuwa g atashin hanklai a tsakanin al’ummar musulmi da sauran al’ummomin duniya.

Bilhasali ma shi addinin muslunci yana kiran dukkanin mutane ne zuwa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma fahimtar juma, duk domin kawai a zauna lafiya.

Haka nan kma malamin ya yi kira ga malamai da masana daga cikin msuulmi da su mike domin fadar da musulmin hakiaknin abin da addininsu yake ira gare shi, tare da kauce sabbin akidoji masu kira zuwa ga ta’addanci da bata sunan muslunci a idon sauran al’ummomin dniya,

Kamar yadda kuma ya yi kira ga masanan da kuma malamai da su zam masu isar da hakikanin sahihin sako na adini ga sauran al’ummomi.

Abdulrahman Sawa Zahab dais hi ne sohon shugaban kasar Sudan kuma mamaba kwamitin masana musulmi wanda Ahmad Tayyib shugaban cibiyar Azahar yake jagoranta.

An kafa wannan kwamiti ne a cikin shekara ta 2014 a birnin eneva, kuma babbar cibiyar kwamitin na birnin Abu Dhabi na kasar UAE a halin yanzu.

3534741


captcha