IQNA

Kofi Annan Ya Ziyarci Yankunan Musulmi A Myanmar

22:42 - December 02, 2016
Lambar Labari: 3480996
Bangaren kasa da kasa, tsohon babban sakataren majlaisar dinkin duniya Kofi Annan ya kai ziyarar gane wa idoa yankunan musulmin kasar Myanmar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaqna cewa, ya nakalto daga Reuters cewa, Kofi Anann ya kai ziyara a yankin Rakhin ta arewa inda a nan mafi yawan musulmin kabilar Rohingya suke.

Yankin dai yana cikin yanayi mafi muni, sakamakon irin matakan da sojojin kasar suka dauka na yin kisan kiyashi a kan faraen hula musulmi yan kabilar ta Rohingya, baya ga munanan ayyuka na fyade a kan matansu.

Kofi Anann ya gana da wasu daga cikin manyna kabilun yankin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, dangane da halin da ake ciki, inda ya bukaci gwamnan lardin da ya dauki matakan da suka dace domin kare rayukan fararen hula da ake yi wa kisan kiyashi a yankin.

Wasu daga cikin mabiya addinin Busda sun nuna rashin jin dadinsu da wannan ziyara ta Kofi Annan a yankin, inda suke ganin cewa hakan zai kara baiwa yan kabilar Rohingya halascin zama akasar.

Musulmin kasar Myanmar dai suna fuskantar matsaloli na kabilanci da kuma banbancin addaini a kasar, sakamakon su ne marassa rinjaye, inda gwamnatin kasar tare da masu tsatsauran ra'ayin buda suk kashe su.

3550264


captcha