Masallacin Tokyo Hasumiyar Musulunci A Japan
Masallacin Tokyo daya ne daga cikin gine-gine na musulunci masu kayatarwa. Wannan wurin ibada mai doguwar hasumiya an gina shi ne bisa tsarin ginin tsohuwar daular Usmaniyya, mai kama da masallacin Istanbul ko (masallacin Sultan Ahmad).