IQNA

Jama'a Na Neman A Zartar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Ci Zarafin Annabi (SAW)

23:51 - December 18, 2016
Lambar Labari: 3481047
Bangaren kasa da kasa, Dubban al'umma ne suka gudanar da jerin gwano a birnin Nuwakshot na kasar Mauritaniya, da ke nemana zartar da hukuncin kisa kan mutumin da ya ci zarafin ma'aiki (SAW) a kasar.
Jama'a Na Neman A Zartar da Hukuncin Kisa Kan Wanda Ya Ci Zarafin Annabi (SAW)

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Middle east MENA cewa, dubban mutanen suka gudanar da jerin gwanon, inda suke bukatar ganin babban kotun kolin kasar ta tabbatar da hukuncin da aka yanke kan Muhammad Sheikh Wuld Ummu Khaitir, mutumin da ya rubutun batunci a kan manzon Allah (SAW) a yanar gizo.

Masu zanga-zangar sun yi ishara da da cewa, tsarin shari'a a kasar ya ginu ne a kan mazhabar Malikiyyah, kuma hukuncin wanda ya ci zarafin manzon Allah a wannan mazhaba shi ne ya yi ridda idan musulmi, kuma za a zartar da hukuncin kisa a kansa.

Manyan malamai da dama a kasar ta Mauritania dai sun amince da kiraye-kirayen da jama'a ke yi na neman ganin an zartar da hukuncin a kan wannan matashi, wanda ya yi batunci ga manzo a cikin watan Disamban 2014.

Babbar kotun kasar ta Mauritaniya ta sanar da cewa ta amince da hukuncin da kotu ta yanke a kansa, kuma za a zartar da shi domin ya zama darasi ga duk wani mai yunkurin yin haka a nan gaba a kasar.



3554456



captcha