IQNA

Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Kakkausar Murya Kan Kisan Jakadan Rasha A Turkiya

23:46 - December 20, 2016
Lambar Labari: 3481051
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Hizbullah ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da kisan jakadan kasar Rasha a Turkiya Andrey Karlov, tare da bayyana hakan a matsayin aikin ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, kungiyar ta Hizbullah ta fitar da bayanin nata adaren jiya, wanda a cikinsa ta bayayna cewa, tana yin tir da Allawadai da kisan jakadan Rasha a Turkiya, kuma hakan ya kara tabbatar wa duniya irin halin da ake ciki na rashin tsaro a yankin saboda matsalolin ta'addanci da aka haifar, wanda hakan ke barazana ga kowa a yankin.

Bayanin ya ce wannan kara tabbatar da cewa wajibi ne a yi yaki da ta'addanci da 'yan ta'adda a duk inda suke, kuma manufar 'yan ta'addan kan kisan jakadan Rasha ita ce kashe gwaiwar kasar Rasha kan yakin da take yi da ta'addanci, amma hakan tabbas babu abin da zai kara ma Rasha sai azama da shiga kafar wando daya da 'yan ta'adda a Syria.

Daga karshe kungiyar Hizbullah ta mika sakon ta'aziyya da alhini ga gwamnatin kasar rasha, da kuma iyalan jakadan na Rasha a Turkiya Andrey Karlov.

3555216


captcha