IQNA

23:22 - January 09, 2017
Lambar Labari: 3481119
Bangaren kasa da kasa, rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani da marecen jiya lahadi ta shiga muhimman kafafen watsa labarun Duniya.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, hakika rasuwar Ayatullah Hashimi Rafsanjani da marecen jiya lahadi ta shiga muhimman kafafen watsa labarun Duniya.

Kafafen watsa labarun kasar Italiya na daga cikin na farkon da su ka watsa labarin Rasuwan Ayatullah Rafsanjani, jim kadan bayan da aka yi sanarwa a Iran.

A kasar Faransa ma labarin rasuwar Ayatullah Rafsanjanin ta shiga cikin muhimman kafafen watsa labarunsu da su ka hada da jaridar Lo Figaro, wanda ta bayyana da cewa daya ne daga cikin muhimman wadanda su ka taka rawa a jamhuriyar musulunci.

A kasar Spain ma muhimman kafafen watsa labarunsu da su ka hada da El Mondo da A.b.c. sun dauki rahotanni na musamman akan rasuwar shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci.

A kasar India kafafen watsa labarunta sun bayyana shi da cewa daga ne daga cikin muhimman mutane masu tasiri a cikin Iran.

A jiya lahadi ne dai Allah ya yi wa Hashimi Rafsanjani rasuwa yana dan shekaru tamanin da biyu  sanadiyyar ciwon zuciya.

3561024


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: