IQNA

21:25 - January 10, 2017
Lambar Labari: 3481122
Bangaren kasa da kasa, Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ce za ta dauki matakai na mayar da martani kan kisan sojojinta da wani bafaletine ya yi a cikin birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar ministocin haramtacciyar kasar Isra'ila ta gudanar karkashin jagrancin Benjamin Netanyahu, ta yanke shawar daukar wasu kwararan matakai kan Falastinawa sakamakon halaka sojoji 4 da Fadi Ahmad Hamdan Kanbar ya yi.

Isra'ila ba ta bayyana matakan ba, amma tuni ta yi umarnin da a rushe gidan Fadi Ahmad, kuma ta kame danginsa da suka hada da mahaifansa da 'yan uwansa na jini, kuma ba a san halin da suke ciki ba, yayin da ake sa ido a kan falastinawa.

Haka nan kuma firayi ministan haramtacciyar kasar yahudawan ya bayyana cewa, ba za susake yin sake da irin wadannan ayyuka da ya kira na ta’addanci su ci gaba da faruwa a kan yahudawa ba.

Wannan baflastine dai ya kai harin ne da nufin daukar fansa kan irin cin zarafin da yahudawa suke yi kan al’ummar Palastine na kisan gilla da kuma rushe musu gidaje da bata musu kaddarori.

A lokacin da ya kai harin da babbar motar daukar kaya, ya yake sojojin yahudawa ashirin, inda ya kasha hudu, ya kuma jikkata wasu sha biyar, inda yanzu haka wasu sha hudu suke asibiti.

3561232


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: