IQNA

19:25 - January 11, 2017
Lambar Labari: 3481123
Bangaren kasa da kasa, a yau ne aka fara zaman ta'aziyyar Ayatollah Hashimi Rafsanjani a Husainiyyar Imam Khomeni (RA) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a zaman ta'aziyar, dangin marigayin tare da manyan jami'an gwamnatin Iran da suka hada da shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokoki gami da babban alkalin alkalai, gami da sauran dubban mutane daga ko'ina da suke halartar wurin.

A farkon zaman dai an bude wurin da karatun kur'ani mai tsarki, da kuma karato wasu daga cikin bayanai na manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

A jiya ne dai aka gudanar da janazar Ayatollah Hashimi Rafsanjani, wanda jagoran juyin juya halin muslunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya jagoranta, an kuma bizne gawar tasa ne a cikin hubbaren marigayi Imam Khomenei (RA) da ke kudancin birnin Tehran.

Ayatollah Rafsanjani dai ya rike mukamai da dama a kasar Iran, kamar yadda kuma ya taka gagarumar rawa wajen kafuwar juyin juya halin muslunci a Iran.

3561583

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: