Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Shafin yada labaran WB ya habarta cewa, an bude wuta a kan mutanen biyu ne wadanda dukkaninsu mabiya addinin hindus ne da suke zaune a jahar Texas ta Amurka, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikinsu a nan take, wanda injiniyan ayyukan gyaran hanya ne da ke aiki tare da wani kamfanin kwangila na kasar ta Amurka, yayin da dayan kuma yake rai hannun a asibiti.
Jami'an 'yan sanda na jahar Texas sun ce sun kame wani mutum dan shekaru 51 da a samu da bindiga a lokacin da abin ya faru, kuma a ji yana cewa da mutanen biyu su koma kasarsu ta asali, kafin daga bisani kuma a ji harbin bindiga.
Mutumin da aka kame dai yaki amsa laifinsa, amma shedun gani da ido sun tabbatar da cewa shi ne ya aikata wannan aika-aika, a akan haka zai fuskanci hukuncin kisan kai da kuma hukuncin yunkurin yin kisan kai na biyu.
Kyamar musulmi a kasar Amurka na ta kara ta'azzara tun bayan da Donld Trump ya lashe zaben Amurka