IQNA

Likitocin Isra'ila Na Azabtar Da Palastinawa A Kurkukun Isra'ila

23:52 - March 05, 2017
Lambar Labari: 3481287
Bangaren kasa da kasa, an zargi likitocin haramtacciyar kasar Isra'ila da azabtar da Palastinawa da suke tsare a cikin kurkukun Isra'ila ta hanyoyi da daban-daban.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran WB ya bayar da rahoton cewa, kwamitin da ke kula da lamurran palastinawa da Isra'ila ta kame kuma take tsarea gidajen kurkukunta ya fitar da bayani da ke tabbatar da cewa, likitocin yahudawan sahyuniya tare da hadin gwiwa da masu gadin gidajen kason Isra'ila, suna azbatar da palastinawa da ake tsare da su.

Bayanin ya ce daga cikin hanyoyin azabtarwar kuwa har da hana su magunguna alokacin da ba su da lafiya, da kuma gaya masu magnganu na bacin rai da ka iya jefa rayuwar palastinawa marassa lafiya cikin wani hali.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, jami'an tsaron gidajen kason suna azabtar da palastinawa da suke tsare da su, tare da hadin gwiwa da likitocin da aka kawo domin su musu magani, kuma hakan na faruwa ne tare da sanin mahukuntan Isra'ila.

Tun bayan fitar da wannan rahoto dai a jiya, har yanzu jami'an haramtacciyar kasar Isra'ila ba su ce uffan ba.

3580793

captcha