Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya dubban Palastinawa sun fito a yankuna da daman a gabar yamma da kogin Jordan da gabashin birnin Quds domin nuna rashin amincewa da hana musulmi gudanar da kiran a cikin birnin Quds.
A yayin jerin gwanon an daga kyallaye masu dauke da rubutu da nuna rashin amincewa da amincewar da majalisar haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi da daftarin kudirin da aka mika mata.
Wannan daftarin kudiri wanda gwamnatin yahudawan sahyuniya ta shirya, ya bukaci da a haramta gudanar da kiran salla a birnin Quds da hakan ya hada har da masallacin Aqsa mai alfarma.
Malaman addini da masana a kasashen duniya daban-daban suna ci gaba da yin tir da Allawadai da wannan mataki, wanda yake a matsayin cin zarafi da tozarci ga dukkanin musulmi na duniya.
Masallacin Aqsa yana a matsayin masallaci na uku mafi daraja a wurin musulmi, bayan masallacin haramin Makka, da kuma masallacin manzon Allah (SAW) da ke Madina.