IQNA

Taron Maulidin Sayyidah Zahra (SA) A London

23:43 - March 16, 2017
Lambar Labari: 3481317
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron maulidin Sayyidah Zahra (AS) a cibiyar muslunci da ke birnin London na kasar Birtaniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ic-el.com cewa, za a gudanar da taron maulidin syiidah Zahra a cikin harshen farisanci da larabcia babbar cibiya mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da ke birnin London.

Bayanin ya ce, wannan taro zai samu halartar musulmi daga dukkanin bangarori na mabiya ahlul bait (AS) da kuma sauran bangarori na musulmi, domin jin bayani a kan shugabar mata na duniya da lahira.

Sayyid Jafar Musawi zai gabar da jawabi a wurin taron, kamar shi ma Sayyid Abdulmun’im Muhammad Hassan shi ma zai gabatar da nasa jawabin a cikin harshen larabci.

Babban abin jawabin zai mayar da hankali a kansa shi ne, matsayin sayyidah Zahra (SA) da kuma darussan da ke cikin rayuwarta wadanda abin koyi ne ga dukkanin musulmi.

3584677

captcha