IQNA

An Bude Gasar Kur'ani Mai Tsarki A kasar Lebanon

21:19 - March 23, 2017
Lambar Labari: 3481339
Bangaren kasa da kasa, an bude gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar Lebanon tare da halartar mayna jami'an gwamnatin kasar da kuma malamai.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya bayar da rahoto daga birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon cewa, an bude wannan gasa ne a masallacin Muhammad Alamin da ke birnin na Beirut.

A yayin bude gasar an samu halartar Najib Mikati tsohon firayi ministan kasar, da kuma Sa'ad Hariri Fira minister na yanzu, da kuam Fu'ad Senura tsohon fira minister da kuma Tamam salam gami da Abdullatif daryan babban mai bayar da fatawa na gwamnatin kasar.

Wannan gasa dai na daga cikin gasar kur'ani da aka saba gudanarwa a kasar ta Lebanon tare da halartar malamai da kuma jami'an gwamnati, gami makaranta daga sassa na kasar da ma wasu daga cikin kasashen larabawa.

Wannan gasa na mayar da hankali a bangaren karatu da hukunce-hukuncensa da kuma wasu daga ilmomin tafsiri, kamar yadda kuma akan taba bangaren harda.

3585381

captcha