IQNA

Kalubalantar Kyamar Musulmi A Kasar Amurka

22:04 - March 25, 2017
Lambar Labari: 3481345
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri a jami'ar Minnesota ta kasar Amurka domin kalubalantar siyasar kymar musulmi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an shirya gudanar da wannnan shiri bayan ganin irin karuwar kyamar msuulmi da ake samua kasar Amurka tun bayan da Donald Trump ya dare a kan kujerar shugabancin kasar.

Salon siyasar kyamar musulmi na daga cikin abin da Trump ya yi amfani da shi wajen yakin neman zabe, inda masu tsananin adawa da musulmi suka shiga gaba domin ganin sun mara masa baya har ya kai cin nasarar wajen samun wakilai fiye da abokiyar karawarsa, wadda ta zarta shi da kuri'u.

Taron dai zai gudana ne yau tare da halartar masana da malaman jami'oi gami da wakilan kungiyoyin da ke rajin kare hakkin bil adama.

Khedr Khan kamahaifin Hamayun Khan sojan Amurka musulmi da aka kasha a kasar Iraki zai gabatar da jawabi a wajen taron nay au.

Babbar manufar taron dai ita ce samar da hanyoyin kalubalantar bakar siyasar wariya da kymar wani jinsin bil adama saboda dalilai na banbancin addini, wanda gwamnatin Amurka take tafiya a kansa a halin yanzu a hukumance.

Da dama daga cikin Amurkawa dai basu amince da salon siyasar Trump ba, domin kuwa har yanzu ana gudanar da jerin gwano da zanga-zangar nuna rashin gamsuwar da siyasarsa ta wariya da kin baki.

3585613
captcha