IQNA

Wani Jami’in Gwamnatin Belgium Ya Kare Hukuncin Hana Saka Hijabi A Turai

23:48 - March 26, 2017
Lambar Labari: 3481349
Bangaren kasa da kasa, wani babban jami’in gwamnatin kasar Belgium ya fito yak are hukuncin da kotun tarayyar turai ta yanke kan hana mata musulmi saka hijabi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Anatoli cewa, jami’in mai mukamin minister a cikin gwamnatin Belgium ya nuna gamsuwa matuka da hukuncin babbar kotun tarayyar turai na bayar da dama ga kamfanoni su hana mata msuulmi saka hijabi a cikin wuraren ayyukansu.

Zahar Dmir wanda shi ne ministan kare hakkin bil adama na kasar Belgium ya bayyana cewa, ko shaka babu wannan ba sabon batu ba ne, domin kwa an gabatar da wanann Magana tun kimanin shekaru 20 da suka gabata, amma ba dauki wani hukunci ba sai yanzu.

Ya kara da cewa, da a ce tun lokacin an dauki irin wannan hukunci, to an samu saukin matsalolin da ake fuskanta a cikin nahiyar turai,sakamakon yadda musulmi suka cika nahiyar ahalin yanzu, wanda a cewarsa ya zama babbar barazana ta tsaro kasashen nahiyar.

Sai da dama daga cikin masa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama a cikin kasashen anhiyar turan suna kallon haka a matsayin wani mataki na tauye hakkokin bil adama, domin kuwa musulmi mutane ne kamar kowa, suna da hakkin su kiyaye lamurran da addininsu ya lizimta musu, matukar dai hakan baya na cutar da sauran al’umma ba ne.

3585728

captcha