IQNA

An Zartar Da Hukuncin Kisa A Kan Jagoran Kungiyar Jihad Islami A Bangaladesh

20:25 - April 14, 2017
Lambar Labari: 3481405
Bangaren kasa da kasa, an zartar da hukuncin kisa a kan jagoran kungiyar Jihad Islami a kasar Bangaladesh bisa zargin bude wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar wuta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, ministan cikin gida na kasar Bangaladesh Asadu Zaman Khan ya sanar da cewa, an zartar da hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhanan, jagoran kungiyar Jihad Islami, tare da wasu mutane biyu na hannun damarsa, bisa samunsu da hannu a harbin da aka yi wa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh.

Tun kimanin shekaru 12 da ska gabata ne dai ‘yan kungiyar ta Jihad Islami suka budewa tsohon jakadan Birtaniya a kasar Bangaladesh wuta, amma bas u samu damar kasha shi, sai dai jami’an ‘yan sanda 3 sun rasa rayukansu,yayin da wasu mutane 79 suka samu raunuka.

Tun a cikin shekara ta 2014 ne dai wata kotu ta yanke hukuncin kisa a kan Mufti Abdulhannan tare da wasu na hannun damarsa, tare da yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu 6 daga cikinsu.

3589444

captcha