IQNA

Jeirin Gwanon Amurkawa Domin Nuna Goyon Baya Ga Musulmi

23:59 - April 27, 2017
Lambar Labari: 3481444
Bangaren kasa da kasa, daruruwan Amurkawa ne a birnin Door na jahar Delaware suka gudanar da jirin gwano domin nuna goyon bayansu ga msuulmi.

Kamfanin dillancin labarran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na Delaware State News cewa, wannan jerin gwano ya samu halartar dukkanin bangarori na jama’ da suka hada har da sojoji da kuma ‘yan sanda.

Babbar manufar shirya wannan jerin gwano dai ita ce nuna rashin amincewa da irin matakan da wasu Amurkkawa suke dauka a kan musulmi na nuna musu tsangwama da kyama.

Da dama daga cikin wadanda suka shiga wannan jerin gwano dai ba musulmi ba ne, amma kuma suna nuna takaicinsu matuka dangane da abin da ake yi wa musulmi na batunci.

Kyamar msuulmi ta karu a kasar Amurka ne tun bayan da Donald Trump ya dare kan kujerar shugabancin kasar, wanda kuma daya daga cikin abubuwan da ya yi kamfe da su shi ne kin jinin musulmi da kuma nuna musu tsangwama.

A karshen jerin gwanon gwamnan jahar Delaware John Carny ya gabatar da takaitaccen jawabi, inda ya bayyana cewa musulmi da wand aba usulmi duk ‘yan ada ne kuma dole a kare mutuncinsu da zarafinsu a ko’ina ne, saboda haka ba zai taba amincewa da takura ma musulmi ba.

3593693


captcha