Masallacin Tur Sina Wurin Musulmin Ethiopia
Masallacin Tur Sina yana yankin Wello a arewacin Ethiopia. Wannan masallaci an yi shi ne daga katako, yana a matsayin daya daga cikin muhimman wurare na tarihi na musulmi a wannan kasa ta Ethiopua. Masallacin Tur Sina dadden wuri ne da aka yi amfani da fasaha ta musamman ta aikin katako domin gina shi.