IQNA

Ranar Karshe Ta Gasar Kur'ani Mai Tsarki A Malaysia

20:00 - May 19, 2017
Lambar Labari: 3481529
Bangaren kasa da kasa, a yau ne ake kawo karshen gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki karo na hamsin da tara a kasar Malaysia a ginin babbar cibiyar putra da ke birnin Kuala Lumpur inda Hamed Alizadeh zai yi karatu

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto daga birnin Kuala Lumpur cewa, daren yau ne na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki karo na hamsin da tara a kasar Malaysia a ginin babbar cibiyar putra da ke birnin Kuala Lumpur.

Mubarak Taleb daga Afirka ta kudu zai karatu daga aya ta 91 surat Muminun, Nur Muhammad Bin Ali daga Singapour daga aya ta 95 surat An'am, Jeljinr Irili daga Kazakhstan, Muhammad Ayyub Asef daga Ingland daga aya ta 77 Ma'idah, Wan Fakhrurazi bin Wan Muhammad daga Malaysia aya ta 80 surat A'araf, Iman Al-zutni daga Morocco, Hamed Alizadeh, Hussain Taher Shaker Albarzanji daga Iraki, aya ta 1 surat A'araf.

Kimanin karfe 19 na daren yau Hamed Alizadeh daga Iran zai karatu a wurin gasar, inda zai kara da takwarorinsa daga Ingland da kuma Malaysia.

Karatun (Mubarak Taleb) Afirka ta kudu

Saurare

Karatun )Nur Muhammad Bin Ali) Singapour

Saurare

Karatun (Muhammad Ayyub Asef) Ingland

Saurare

Karatun (Wan Fakhrurazi bin Wan Muhammad) Malaysia

Saurare

3601039


captcha