IQNA

Sayyid Mustafa Husaini Daga Iran ya Zo Na Daya A Gasar Kur’ani A Turkiya

23:09 - May 24, 2017
Lambar Labari: 3481544
Bangaren gasar kur’ani, Sayyid Mustafa Hussaini dan kasar Iran ya zo na daya a gasar kur’ani ta duniya da aka gudanar a kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Sayyid Mustafa Hussaini daga kasar Iran ya zo na daya a bangaren kira’a a gasar kur’ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar karo na biyar a kasar Turkiya.

Makaranta da mahardata 120 ne daga kasashen duniya 62 suka gudanar da wannan gasa a bangarorin tilawa da kuma harda.

A yammacin yau ne za a gudanar da taron rufe gasar tare da halartar manyan jami’ai da kuma malamai, tare da bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.

3602845


captcha