IQNA

Abubuwa Da Suke Hada Musulmi Da Kirista A Watan Ramadan A Masar

23:43 - May 25, 2017
Lambar Labari: 3481548
Bangaren kasa da kasa, akwai abubuwa da dama da suke hada msuulmi da kiristoci a wuri guda a cikin watan Ramadan mai alfarma a kasar masar

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Alwafd cewa, a cikin watan Ramadan mai alfarma musulmi da kiristocia kaar sukan gudanar da abubuwa da dama tare, domin karfafa dangantaka a tsakaninsu.

Daga muhimman abubuwan da suke yi akwai cin abincin buda baki a tare a wuraren ayyuka ko masallatai, ko kuma a manyan wuraren cin abinci, inda sukan ci abinci tare da tare da taya juna murnar azumin watan Ramadan mai alfarma.

Bayanin ya ci gaba da cewa sau da yawa mabiya addinin kirista sukan shirya wa msuulmi buda baki a gidajensu ko kuma a wuren ayyuka, domin kara tabbatar da dankon zumunci da zaman lafiya da ke tsakaninsu.

Kamar yadda su ma musulmi sukan shirya irin wadannan taruka na buda baki tare da gayyatar musulmi da kiristoci domin cin abinci a tare, lamarin da ya samo asali tun tsawon daruruwan shekaru.

Irin wannan lamari yana da matukar tasiri wajen karfafa zumunci da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al'ummar kasar Masar musulmi da kiristoci.

3602548


captcha