IQNA

Wakafin Sunni A Iraki Ya Sanar Cewa Gobe Asabar Ranar Farko Ta Ramadan

23:32 - May 26, 2017
Lambar Labari: 3481552
Bangaren kasa da kasa, wakafin sunni a kasar Iraki ya sanmar da cewa gobe Asabar ce ranar farko ta watan azumin Ramadan mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na shafaqana cewa, a gobe ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma ga mabiya tafarkin sunni a Iraki.

Bayanin ya ce bisa ga lissafin watan sha’aban yau juma’a lissafin ya cika talatin daidai akan hakan gobe ne daya ga watan Ramadan mai alfarma.

Babban jami’in ‘yan sanda na lardin Dayala janar Jasim Sa’adi ya bayyana cewa, an ware jami’an kimanin dubu bakawai da za su gudanar da ayyukan tsaro a lokacin azumia cikin wannan lardi, domin bayar da kariya ga jama’a a awuraren tarukan addini da saurans.

Babbar manufar kafa wannan runduna dai ita ce tabbatar da tsaroa lokacin da musulmi suke gudanar da ibadar azumi, ganin yadda kasar Iraki ke fuskantar barazanar ta’addancin wahabiya ‘yan takfiriyya da ke kai hare-harea cikin kasar.

Kasashen musulmi da dama dai daga gobe ne za su tashi da zumin watan Ramadan mai alfarma, musamman ma wadanda lissafinsu na watan sha’aban ya cika yau talatin daidai.

3603294


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha