Hamed Alizadeh wanda ya lashe gasar karatun kur'ani mai tsari ta duniya da aka gudanar a Malaysia,a zantarwarsa da kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayyana cewa, sun gana da jagora, kuma ya yaba da karatunsa.
Ya ce jagora ya taya shi murna dangane da lashe gasar kur'ani ta duniya da ya yi a Malaysia, inda kuma ya ce da shi zuwa na farko a gasar kur'ani ba shi ne kawo karshen karatun kur'ani ba da kuma ci gaba da kokari.
Haka nan kuma ya ce jagora ya karfafa masa gwiwa da cewa kada ya yi sanyi da karatun littafin Allah, ya ci gaba da kokari, da yin karatu a tarukan jama'a a garinsu da sauran
urare, domin karfafa al'umma a kan sha'anin kur'ani.