IQNA

Kula Da Makarantun Addini Zai Koma Ga Bangare Na Musamman A Ghana

23:50 - May 28, 2017
Lambar Labari: 3481560
Bangaren kasa da kasa, za a mika sha'anin tafiyar da makarantun addinin muslunci ga wani bangare na musamman a kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Matthew Opoku Prempeh ministan ilimi na kasar Ghana ya bayyana cewa, an dauki wannan kudiri ne bayan kafa sabuwar gwamnati a kasar.

Ya ci gaba da cewa, makarantun addini suna daidai da sauran dukkanin bangarori masu matukar muhimmanci da suke cin gishin kansu, kamar kungiyoyin lauyoyi likitoci da asibitoci masu zaman kansu da kuma kungiyoyin ma'aikata.

A kan ya ce ma'iakatarsa za ta mayar da makarantun addini su zama suna da damar gudanar da ayyukansu da harkokinsu cikin 'yanci, ta yadda za a kirkiro wani bangare wanda kawai zai rika zama mai tuntuba tsakaninsu da bangaren zartarwa.

Tun a cikin shekara ta 2014 majami'iun kiristoci suka bayar da shawar cewa ya kamat makarantun addini su zama suna cin gishin kansu ta fuskokin tsari da tafiyarwa, duk da cewa hakan ba zai hana gwamnati daukar nauyinsu ta fuskancin kudade ba.

3604127


captcha