IQNA

Addinin Muslunci Na Yaduwa Cikin Sauri A Madagaska

19:33 - June 01, 2017
Lambar Labari: 3481570
Bangaren kasa da kasa, wani bincike ya tabbatar da cewa addinin muslunci ya kara yaduwa a tsibirin madagaska a cikin shekaru 7 da suka gabata.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Milligazete cewa, karuwar yawan musulmi da aka samu a cikin shekaru bakwai da suka gabta ya fi na kowane lokaci a tarihin tsibirin.

Sakamakon binciken ya nuni da cewa, cikin 'yan shekarun baya-bayan nan adadinin musulmin tsibitrin ya tashi daga kashi 1.1 zuwa kashi 15 cikin dari, a cikin al'ummar wadanda yawansu ya kai milyan 25.

Jin Jack Rwana daya ne daga cikin wadanda suka karbi addinin muslunci a wannan tsibiri a cikin 'yan shekarun da suka gataba, wanda ya bayyana cewa, a baya ya kasance mabiyin addinin kirista, amma daga bisani bayan gudanar da bincike, ya karbi addinin muslunci a matsayin addininsa.

Ya ce babban abin da ya burge shi dangane da addinin muslunci shi ne, baya ga karfafa dan adam ta fuskar ruhi, yan ada tsare-tsare a cikin dukkanin bangarorin rayuwar mutum, a bangaren zamantakewa, siyasa, tattalin arziki, cinikayya da dai sauransu.

Ya kara da cewa, akwai wadanda suke kallon addinin muslunci a matsayin addinin da yake yada ayyukan ta'addanci da kisan kai, amma sakamakon binciken da ya gudanar a kan muslunci, ya fahimci cewa masu aikata ayyukan ta'addanci da kisan jama'a da sunan addinin muslunci ko jihadi, sun yi wa muslunci mummunar fahimta, kuma abin da suke yi ba shi da wata alaka da addinin muslunci.

captcha