IQNA

Ma’aikatar Harkokin wajen Iran Ta Yi Allawadai Da Harin Kabul

23:52 - June 16, 2017
Lambar Labari: 3481615
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da harin ta’addancin da aka kai a birnin Kabul na kasar Afghanistan a cikin masallaci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran bahram Kasimi ya bayyana harin na msallacin Kabul da cewa aiki ne na dabbanci da rashin iamni.

Kasimi ‘yan ta’adda ba su da wata akida ta wani addini, domin kuwa akidarsu ita ce kisan dan adam ba tare da la’akari da addininsa ko akidarsa ba, domin su ba su da addini.

A daren Juma’a ne wasu ‘yan ta’ada masu dake da akidar kafirta musulmi suka kai harin bam a cikin masallaci na mabiya mazhabar shi’a a lokacin da ake gudanar da sallolin daren lailatul kadari, inda suka kasha tare da jikkata mutane da dama.

3610150


captcha