IQNA

Musulmin Jamus Za Su Yi Jerin Gwanon Nisanta Kansu Da ‘Yan ta’adda

0:01 - June 17, 2017
Lambar Labari: 3481617
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Jamus za su gudanar da jerin gwano domin nisanta kansu daga ‘yan ta’adda masu aki hare-hare da sunan addini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau musulmin kasar Jamus za su gudanar da gagarumar zanga-zanga domin tabbatar wa duniya cewa ‘yan ta’adda da ayykansu ba su da wata alaka da musulmci.

Wannan zanga-zanga za ta guda ne abirnin Cologne na Jamus tare da halartar dukkanin kungiyoyin musulmi, amma wata babbar kungiyar musulmi ta Turkawa ta DITIBmai alaka da gwamnatin Turkiya ta ce ba za ta shiga wanann zanga-zanga ba.

Babbar cibiyar musulmi ta kasar Jamus dai ta amince da wannan zanga-zanga, inda ta bayar da umarnin cewa za a iya gudanar da ita ta hanyar llumana domin nisanta muslunci da ‘yan ta’adda masu dauke da akidar nan ta kafirta musulmi da suke kai hare-hare da sunan addinin muslunci suna bata wa musulunci suna.

3610160


captcha