IQNA

An Samu Wani Kwafin Kur’ani Da Za A Yi Fsa Kwabrinsa A Masar

23:52 - June 18, 2017
Lambar Labari: 3481620
Bangaren kasa da kasa, jami’an hukumar da ke kula da shige da ficen kayyakia filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira a Masar ta kame wani kur’ani da za a yi fasa kwabrinsa.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri yaum cewa, Ahmad Rawi shugaban bangaren kula da harkokin kayan tarihi na dukkanin iyakokin Masar ya tabbatar da wannan bayani.

Inda ya ce an samu dauri uku da aka saka wannan kur’ani a kinsu wanda aka rubuta da hannua lokacin mulkin daular Usmaniyya, kuma an shigo da kr’anin ne daga kasar Habasha zuwa kasar ta Masar ba bisa ka’ida ba, saboda haka an kame shi kuma an agudanar da bincike kan lamarin.

Ya kara da cewa, takardun kwafin kur’ani ba ajere suke ba, kamar yadda hatta tsarin surorin ba daidai suke ba, lamarin da ke nuni da cewa wadanda suke da shi bas u san kan yadda tsarinsa yake ba, lamarin da ya kara saka shakku a kan manufar wannan fasa kwabri.

Kasar masar dai na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da ake samun irin wadanna ayyuka na fasa kwabrin kayan tarihi, wadanda suka shafi lokacin tarihin kasar a dubban shekaru da suka gabata, da kuma wasu kayan tarihin muslunci na daruruwa shekaru.

3610797


captcha