IQNA

Wani Babban Kwamandan ISIS Ya Halaka A Harin Da Iran Ta Kai A Syria

22:07 - June 19, 2017
Lambar Labari: 3481623
Bangaren kasa da kasa, Daya daga cikin manyan kwamnadojin kungiyar 'yan ta'addan takfiriyya ta (Daesh) ISIS ya halaka sakamakon harin da Iran ta kaddamar a jiya a kan sansanonin 'yan ta'adda a Syria.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, wasu majiyoyi masu tushe daga fagen daga a kasar Syria sun tabbatar da cewa, Sa'ad Al-husaini dan kasar Saudiyyah, wanda aka fi sani da Abu Sa'ad, daya daga cikin manyan jagororin kungiyar ISIS, yana daga cikin manyan kwamandojin kungiyar 'yan ta'addan na ISIS da suka halaka a daren jiya, bayan saukar makaman ballistic da dakarun IRGC suka harba daga cikin kasar Iran zuwa kan sansaninsu da ke Deir Zur a cikin kasarSyria.

Dakarun na IRGC sun ce wannan somin tabi ne na alwashin da suka sha na mayar da martani da daukar fansa a kan harin da kungiyar ISIS ta kai a Tehran, kuma akwai wasu matakan na gaba da suke tafe a kan kungiyar ta ISIS da masu daukar nauyinsu.

Harin na Iran dai ya girgiza dukkanin wadanda suke da hannu a hare-haren da yan ta'addan suka kai a birnin Tehran a kwanakin baya.

3611235



captcha