IQNA

Jami’an Tsaron Isra’ila Sun kame Palastinawa 2 A Yau

16:42 - June 27, 2017
Lambar Labari: 3481649
Bangaren kasa da kasa,a wani farmaki da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai yau a unguwar Abu Dis da ke cikin birnin Quds, sun kame wasu Palastinawa biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashra cewa, sojojin yahudawa sahyuniya sun kai farmakin ne inda suka kae Mahmud Nafez jafal wanda aka sake kwanakin baya da kuma dan uwansa Muhammad Ziyad Jifal.

Yanzu haka dai ba a san makomar wadannan palastinawa guda biyu ba, kuma babu wani dalili da yahudawan suka bayar na kame su, amma kuma hakan ba bakon lamari ba ne ga al’ummar yankin wadanda suka saba ganin bakin zalunci da danniya daga yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila.

Wannan lamari ya zo ne a daidai lokacin da jiragen yakin yahudawan suka kaddamar da wani farmakia yau a kan wani wurinb tsaro a cikin yankin zirin Gaza, inda suka ragargaza wurin baki daya.

Haramtacciyar kasar Isra’I’a tare da cikakken goyon bayan Amurka da wasu daga cikin larabawa ‘yan korenta ayankin gabas ta tsakiya, tana cin karenta babu babbaka akan al’ummar Palastinu marassa kariya.

3613583


captcha