IQNA

Kakakin Ma’aikatar waje:

Ya Kamata Amurka Ta Dauki Darasi / Trump Ba Shi Da Mashawarta

23:39 - July 15, 2017
Lambar Labari: 3481701
Bangaren kasa da kasa, Bahram Qasemi kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya mayar da martani a kan kalaman Trump dangane da Iran a Paris.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga bangaren diplomasiyya na ma’aikatar harkokin Iran cewa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Bahram Qasemi ya bayyana kalaman da Trump ya yi a kan Iran a lokacin ziyararsa a Paris da cewa Trump ya kara tabbatar da cewa ba shi da masu ba shi shawara da suka san siyasa.

Qasemi ya ce Tun kafin kasashen turai Iran ce ta fara yaki da ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya, domin kuwa tun daga lokacin samun nasarar juyin Islama kasar take fuskantar ayyukan ta’addanci da waus kasashe ke daukar nauyin ‘yan ta’adda, amma da karfin ikon Allah ta samu nasara a kansu.

Ya kara da cewa, zargin Iran dataimaka wa ‘yan ta’addan a yankin gabas ta tsakiya da Trump ya yi a bin ban dariya ga duk wanda ya ji hakan, domin kuwa Iran ita ce kasar da ta zama karfen kafa ga ‘yan ta’adda a yankin da kuma kasashen da suka kirkiro ‘yan ta’addadan, duk kuwa da irin goyon bayan da Amurka take baiwa wadannan kasashe saboda maslharta ta siyasa da tattalin arziki.

3618949


captcha