IQNA

Bayar Da Horo Ga Malaman Makarantun Addini A Uganda

23:46 - July 23, 2017
Lambar Labari: 3481729
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri na horar da malaman makarantun addinin muslucni a kasar Uganda wanda karamin ofishin jakadancin Iran ya dauki nauyin shiryawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da wannan shiri ne tare da halartar malaman makarantun addinin muslunci da kuma daraktocin cibiyoyin addini, domin kara samun horo a kan yadda za su ci gaba da kara bunkasa ayyukansu a wadannan wurare.

Babbar manufar wannans hiri na bayar da horo ita ce kokarin ganin makarantun addinin muslunci da kuma cibiyoyin addini na kasar Uganda sun samu ci gaban da ya kamata, domin su rika taka rawa amataki na kasa a dukaknin bangarori na ilimi, na addini da kuma na zamani.

Ali Bakhtiyari shugaban ofishin yada al’adun muslunci na Iran a kasar Uganda ya bayyana cewa, wannan na daga cikin muhimman lamurran da suke mayar da hankali a kansu domin ganin sun taimaka ma musulmi a nahiyar Afirka a dukkanin bangarori na ilimi.

Wannan shiri dai ya samu karbuwa daga dukkanin bangarori na musulmin kasar ta Uganda, ta yadda kowane bangare na masu wakiltarsa a wurin da ake gudanar da wannan taro na bayar da horo karkashin jagorancin ofishin jakadancin Iran a Uganda.

3622031


captcha