IQNA

Allah Ya Yi Wa Muhammad Abdulwahab Tantawi Rasuwa

21:52 - July 26, 2017
Lambar Labari: 3481737
Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi wa fitaccen makarancin kur'ani mai tsarki a kasar Masar Muhammad Abdulwahab Tantawi rasuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Laraba ce Muhammad Abdulwahab Tantawi ra su bayan kwashe shekaru yana hidima ga addini.

An haife shi a cikin shekara ta 1947 a garin Nasimiya a yankin Deqlahiyya akasar Masar, ya yi shekaru kimanin 70 a duniya yana hidima ga kur'ani mai tsarki.

Ya hardace kur'ani mai tsarki tun yana dan shekaru 10 da haihuwa, ida ya yi karatu a garinsu tun yan ada kuruciya, ya zama fitaccen makarancin kur'ani a kasar Masar, daga bisani kuma ya zama fitaccen makaranci a matsayi na duniya baki daya.

Daga bisani ya kasance daya daga cikin mambobin kwamitin alkalan gasar karatu da hardar kur'ani na duniya, inda yak an halarci tarukan gasar kur'ania koina cikin fadin duniya.

Daga cikin kasashen da ya halarta a lokuta daban-daban har da jamhuriyar muslucni ta Iran, inda yak an samu kyakkyawan tarbe daga al'ummar Iran, sakamakon karbuwar da kira'arsa ta samu a tsakanin mutanen kasar Iran.

Baya ga karatun kur'ani da ya yi shuhura da shi, malamin ya shahara da kyawawan dabiunsa a tsakanin jama'a, wanda hakan ya sanya mutum ne da kwa ke kaunarsa.

3623496

captcha