IQNA

An Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Wani Masallaci A Faransa

21:56 - July 26, 2017
Lambar Labari: 3481738
Bangaren kasa da kasa, bangaren da ke sa ido kan kyamar musulmi a cikin kasashen nahiyar turai da ke karkashin kulawar cibiyar Azhar ya yi Allawadai da kan keta alfarmar wani masallaci na musulmi a gabashin kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Shafin yada labarai na jaridar Yaum Sabi a kasar masar ya bayar da rahoton cewa, wasu masu tsananin kiyayya da musulmi a gabashin kasar Faransa sun keta alfarmar wani masallaci.

Wannan bayanin ya zo bayan da musulmi masu salla a masallacin suka isa domin yin sallar asubahi, inda suka iske cewa an raye kawunan aladu a kan kofar masallaci, da nufin muzguna wa musulmi ta wannan hanya.

Bayanin cibiyar da ke karkashin cibiyar Azhar ya bayyana wannan a matsayin daya daga cikin ayyuka na tsokana da kuma nuna kyama ga mabiya addinin muslunci a kasar Faransa da ma wasu kasashen nahiyar turai, wanda hakan ke nuni da cewa kyamar musulmi na karuwa a kasar.

Cibiyar ta ce dole ne gwamnatin Faransa ta dauki matakin bayar da kariya ga msuulmi, domin kare rayukansu da dukiyoyinsu da wuraren ibadarsu da kuma mutuncinsu.

3622484


captcha