IQNA

An Kai Hari Kan Ginin Gidan Radio Na Alkur'ani A Libiya

23:40 - July 29, 2017
Lambar Labari: 3481749
Bangaren kasa da kasa, Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a gidan radion Alkur'ani da ake kira Kimami andalos dake Tripoli babban birnin kasar Libiya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labara na libyaobserver ya bayar da rahoton cewa, jami'an gwamnatin Libiya na cewa duk da cewa maharan sun yi barazanar kisa a kan ma'aikatan gidan radiyon, to ganin cewa sun yi awan gaba da kudaden gidan radion na Kimamil-andalos, hakan ya fayyace mafunarsu na cewa barayi ne.

Kasar Libiya ta fada cikin rikici ne tun bayan da kungiyar tsaro ta Nato ta kifar da gwamnatin marigayyi kanar Mu'amar Kaddafi a shekarar dubu biyu da sha daya.

Kasashen yammacin turai ne suka taka gagarumar rawa tare da yan ta’adda da ke samun goyon bayan wasu sarakunan larabawa wajen kifar da gwamnatin Libya tare da hargitsa kasar.

3623976


An Kai Hari Kan Ginin Gidan Radio Na Alkur'ani A Libiya

An Kai Hari Kan Ginin Gidan Radio Na Alkur'ani A Libiya


An Kai Hari Kan Ginin Gidan Radio Na Alkur'ani A Libiya


captcha