Majalisar musulmin kasar Amurka ta bukaci mahukunta a jahar ta Minnesota da su dauki matakin kama shi da kuma hukunta bisa abin da ya aikata, wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokokin kasar Amurka.
Jama'a da dama ne dai suka sheda abin da mutumin ya aikata, daga cikinsu kuwa har da wani dan sanda, wanda ya bayar da sheda akan cewa lallai mutumin ya ci zarafin musulmi.
Yanzu haka dai kotun jahar Minnesota na shirin gurfanar da wannan mutum domin hukunta a shi a kan laifin cin zarafin dam adam bisa banbancin addini da akida.
Cibiyar musulmin Amurka ta bayar da rahoton cewa, kyamar musulmi a cikin Amurka ta karu da kashi 91 cikin dari a cikin 2017, idan aka kwatanta da shekara ta 2016 da ta gabata.