IQNA

Za A Fara Zaman Makoki A Masallacin Sayyid Shuhada A Los Angeles

17:56 - September 20, 2017
Lambar Labari: 3481914
Bangaren kasa da kasa, za a fara gudanar da zaman makoki a masallacin Los Angeles a yau laraba domin fara shirin shiga watan Muharram.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na masu gudanar da makoki cewa, a daren yau ne za a fara gudanar da zaman makoki a masallacin tare da sauraren bayani daga Sayyid Ruhullah Jidari babban limamin masallacin.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan yana daga cikin irin abubuwan da ake gudanarwa awannan masallacia lokutan bukukuwan Ashura da sauransu, inda aka yi taruka da kuma bayanai kan munasaba.

Wanann masallaci na daga cikin masallatai damabiya afarkin iyalan gidan manzon Allah suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

A daren gudanar da addu'ou akan yi kamar Tawassul, dua Komail dama sauran addu'oi da ake daidai da ranakunsu.

3644184


captcha