IQNA

An Yi Allah Wadai Da Karuwar Kyamar Musulmi A Spain

22:10 - September 22, 2017
Lambar Labari: 3481922
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azhar da ke Masar ta yi kakkausar ska dangane da karuwar kyamar musulmi a cikin kasar Spain a cikin lokutan nan.

Kamfanindillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga jardar Alwatan cewa, bbabbar cibiyar usulunci ta Azhar da ke kasar Masar ta yi kakkausar suka dangane da karuwar kyamar musulmi a cikin kasar Spain a wannan lokaci.

Bayanin ya ce tun bayan faruruwar hare-haren ta’addancin da aka kaddamar a kasar ta Spain akwanain baya, an samu karuwar nuna kyama ga msuulmi ta hanyar cin zarafinsu da kai farmaki a wuraren ibadarsu.

A cikin makonnin wasu amsu gaba da addinin muslunci sun rika yin rubuce-rubuce a kan bangayen masalatai da kuma cibiyoyin musulmi, suna yin kamalamn batunci a kan addinin muslunci da musulmi.

Haka nan kwanain baya wata musulma ta fuskanci cin zarafi daga wani mutum a cikin tasha jiragen kasa a cikin birnin Madrd fadar mulkin kasar, inda wani mutum ya yi ta ihu a lokacin da ta shig, yana cewa basu son ganin musulmi a nan.

A ranakun 18 da 19 ga watan Agusta ne aka kai harin ta’adanci a biranan Barcelona da kuma Kambril, inda mutane da dama suka rasa rayukasu wasu kuma 130 suka samu raunuka, kungiyar daesh ta dauki alhakin kai harin.

3644863


captcha