IQNA

Tattaunawa Tsakanin Mabiya Addinai A Canada

22:41 - September 23, 2017
Lambar Labari: 3481923
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wata tattaunawa da za ta hada mabiya addinai a kasar Canada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na myyellowknifenow ya bayar da rahoton ewa, Bashir Islam daya daga cikin jagororin musulmi a kasar Canada ya bayyana cewa, wannan taro yana da matukar muhimmaci.

Ya ce a wannan zaman taro za a tattauna muhimman batutuwa da za s tamaka waje kara kawo fahimtar una tsakanin dukkanin mabiya addinai na duniya.

Daga cikin wadanda za su halarci tarona kawai mabiya addina yahudanc, kiristanci, buda, Hindus da kuma musulmi, inda za su yi dubi kan muhimman lamurra da suka shafi batun zaman lafiya da kuma fahimta juna.

Ya kara da cewa baya ga mabiya wadannan addinai akwa mabiya addinai na gargajiya a kasa su ma za su halarci taron.

Bisa ga ididdigar da aka bayar a sheara ta 2001, adadin musulmin Canada ya kai kusan rabin miliyon, wato kasa da kashi 2% na dukkanin al’ummar kasar.

3645180


captcha