IQNA

Gwamnatin Myanmar Na Kawo Cikas A Ayyukan Agaji Ga Musulmin Rohingya

16:29 - September 24, 2017
Lambar Labari: 3481929
Bangaren kasa da kasa, Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa: Yawan 'yan gudun hijirar Myanmar ko kuma Burma da suka nemi mafaka a kasar Bengaledesh sun haura mutane dubu dari bakwai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A sanarwar da kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Juma'a ya bayyana cewa: Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun hijirar Majalisar Dinkin Duniya ta amsa kiran mahukuntan kasar Bangaledesh na hanzarta gabatar da tallafin mayafi ga 'yan gudun hijirar Myanmar domin kare su daga matsalar hunturu musamman sakamakon tsananin sanyin da ke kadawa a yankin da aka tsugunar da 'yan gudun hijirar.

Har ila yau Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana tsananin damuwarta kan mummunan halin da 'yan gudun hijirar Myanmar suke ciki a fuskar kiwon lafiya a sansanoninsu da suke kan iyakar Bangaledesh da Myanmar tare da jaddada bukatar hanzatar gabatar da tallafin gaggawa ga 'yan gudun hijirar.

Tun a shekara ta dubu biyu da sha biyu ne sojojin gwamnatin Myanmar ko kuma Burma da hadin gwiwar mabiya addinin Bouza na kasar suka fara kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar musulmin Rohingya da nufin nurkushe su daga kan doron kasa ko kuma korarsu daga kasar, inda a hare-haren baya-bayan nan sukakashe musulmin Rohingya fiye da dubu shida tare da jikkata wasu dubu takwas na daban, baya ga tilastawa wasu dubban daruruwa tserewa daga muhallinsu.

3645793


captcha