IQNA

Za A Bude Makarantun Kur’ani A Cikin Manyan Masallatan Masar

23:19 - September 25, 2017
Lambar Labari: 3481932
Bangaren kasa da kasa, nan ba da jimawa ba za a bude makarantun koyar da karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki a cikin manyan masallatai da ke cikin fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Muhammad Mukhtar Juma’a minister mai kula da harkokin addini a Masar ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a fara aiwatar da wannan sharia cikin fadin kasar ta Masar baki daya.

Ya ce ma’aikatarsa ce za ta dauki nauyin aiwatar da wanann shiri baki daya, kuma za abayar da ilimi kyauta ga dukkanin wadanda suke halartar shirin, kamar yadda kuma za a rika biyan malaman albashi a kowane wata.

Ministan ya yi ishara da cewa, manufa wannan shiri dai ita ce kara yada lamarin kur’ani mai tsarki a tsakanin al’ummar Masar musamman ma dai matasa daga cikinsu.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, makarantun da za a bude a manyan masallatan kasar, limaman juma’na wadannan masalatai za a damkawa nauyin kula da su.

Kamar yadda uma ya bayyana sharudan daukar malamai da za su koyar, daga ciki har da sharadin cewa dole ne malamin ya zama mahardaci, kuma baya da alaka da wata kungiya ta masu tsatsauran ra’ayi.

3646073


captcha